Aƙalla ƴan jarida huɗu ne suka rasa ransu yayin da suke dawowa daga auren ƴar ɗaya daga cikin abokan aiki.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa ƴan jaridar na aiki ne a gidan jarida mallakin jihar Akwa Ibom kuma sun gamu da ajalinsu ne a kan hanyarsu ta dawowa.
Mutane 18 ne suka jikkata kamar yadda shugaban kula da haɗɗura ta ƙasa reshen jihar ya tabbatar, kuma tuni aka garzaya da su asibiti don karɓar magani.
Shugaban kiyaye haɗɗuran Sunday Oghenekaro ya ce hatsarin ya faru ne sanadin wata mota ƙirar bus da ke ɗauke da mutanen da suka zarce ƙa ida kuma suke gudun wuce sa a a titin.


