Hukumar kula da masu yiwa ƙasa hidima NYSC ta tabbatar da cewar masu yiwa ƙasa hidima za su fara cin gajiyar mafi ƙarancin albashi naira dubu 30 daga watan janairun 2020.
Daraktan hukumar Shu aibu Ibrahim ya tabbatarwa da jaridar Premium Times hakan yayin wata tattauna da shi da musamman.
A yanzu dai masu yiwa ƙasa hidimar na karɓar naira 19,800 kowanne wata, kuma daga shekarar 2020 za su fara karɓar naira 30,000 kowannensu kuma a kowanne wata.
Ministan matasa da wasanni Sunday Dare ya tabbatar da cewar shirin na gab da kammala don fara cin gajiyar sabon tsarin.


