Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Kara jaddada Shirin gwamnatin sa na bada nagartaccen ilimi kyauta kuma dole a fadin jihar.

Ganduje na wannan jawabi ne a lokacin da ya ke karbar Shaidar karramawa a matsayin Uba a fannin bada ilimin zamani kuma kyauta na shekarar 2019, daga hannun Shugaban Kungiyar yan jaridun jihar Kano Reshen wakilan bangarori.

Gwamnan ya kuma Kara tabbatar da burinsa na ganin Almajirai ma sun Amfana daga Shirin na bada ilimi kyauta kuma dole tun daga Matakin farko har zuwa sakandare, duk da mafi yawan su ba yan asalin jihar Kano bane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: