Gwamnatin jihar Kano ta hana daukar maza da mata a babura masu ƙafa uku na A Daidaita Sahu a jihar daga farkon shekarar 2020 mai kamawa, a wani yunƙuri na magance rashin ɗa’a.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar ya bayyana haka ranar Laraba a taron Annual Vacation Course, IVC, da Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta Ƙasa, MSSN, Reshen Jami’ar Bayero ta Kano, BUK ta shirya.

Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Kwamanda Janar na Hukumar Hisba, Harun Ibn-Sina, ya ce dalilin hana cakuɗuwar maza da matan shi ne cusa ɗabi’un Musulunci da kuma tilasta aiki da dokokin Musulunci a jihar.

Wakilin gwamnan Ibn sina ya kuma yi kira ga mahalarta taron da su mayar da hankali a kan karatu, su kuma guje wa shan ƙwaya,da sauran ababen sa maye, Wanda hakan ke lalata rayuwar matasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: