Wata gobara da tashi a wani gida dake karamar hukumar Hadeje ta jihar Jigawa tayi sanadin mutuwar wata yarinya mai shekara daya a duniya.

Gobarar da tashi ne a gidan Mal Mohammad Rabi’u Wanda ma’aikaci ne a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Jigawa.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 1:00 na dare Kamar yadda mai magana da yawun jami’an tsaro na Civil Defense Cs Adamu shehu ya shaidawa manema Labarai.

A cewarsa gobarar ta lakume miliyoyin Dukiyoyi da Yarinya guda daya.

Ya kuma kara da cewa anyi nasarar kashe wutan ne da jami’an mu da na kashe gobara sai kuma taimako da muka samu daga Al’umma.