Matasan su biyu abokai masu shekaru 25 a duniya sun rasa ransu bayan wani muku mukun sanyi da yaauku a ƴan kwanakinan.

Matasan mazauna garin Gangare a ƙaramar hukumar Jos North, sun rasa ransu ne a rqnar juma a da daddare bayan sun dawo gida da misalin ƙarfe 11 na dare.

Wani mai suna Alhaji Labiru ɗan uwa ga ɗaya mamacin yabayyanawa jaridar Blueprint cewar, ƙanin nasa tare da abokinsa sun rasu ne a gidansa bayan sun kwanta a ɗakinsu da ke ƙofar gida a ranar juma a.

Sanyin da aka yi a ƴan kwanakinnan ya sa mutane da dama ɗaukar mataki daban daban don ɗumama jikinsu da wuraren da suke zama, a jihar Plateau kuwa sanyin ya kai matakin 6.7 digiri.

Leave a Reply

%d bloggers like this: