Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na digita malam Isa Ali Pantami ya bayyana cewa nan da shekaru 10 masu zuwa na kaso 95 cikin 100 na yan Najeriya za su iya samun ilimin rubutu da Karatu na digital, sakamakon haka ne za a watsar da duk wasu ayyukanyi na kasar.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Juma’a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai game da ayyukan ofishinsa na ICT a Abuja.
A cewarsa, ma’aikatar sadarwa tana shirin fara horar da ‘yan Najeriya game da iya karatu da rubutu da fasahar zamani,tare da tsarin Shugaba Muhammadu Buhari na farfado da tattalin arziki da ci gaban kasa.

“A cewar Pantami Ba muna gaya wa ‘yan Najeriya ne su yi ƙaura zuwa cikin tattalin arzikin digital don fara bada harajin da suke buƙata ba.

“Farashin bayanai, na’urorin hannu dole ne su sauko don tattalin arzikin tsarin Digital ya bunkasa. Mun biya kuɗin tun kafin sauka akan hanyoyi.
” Ana son fara zurfafa horar da ‘yan Najeriya akan harkar karatu da rubutu na fasaha.
Muna son tabbatar da cewa aƙalla kashi 95% na ‘Yan Najeriya sun samu ilimin zamani, tsarin Digital.
Matashiya/Muryar Yanci