Rundunar Sojin kasa ta Najeriya ta bayyana fadan da gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum aka dauke shi yana yi ma Sojoji a matsayin abin da ka iya kashe ma Sojoji kwarin gwiwa, kuma ya mayar da hannun agogo baya ga nasarar da aka samu da Boko Haram.

A cikin wani bidiyo dake yawo a shafukan sadarwa, an hangi gwamnan yana yi wa Sojoji tsawa tare da zarginsu da karbar cin hancin N1000 daga hannun direbobin dake bin babbar hanyar Maiduguri – Dammaturu.
Cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa abin da gwamnan yake yi zai iya kawo tarnaki ga nasarorin da dakarun rundunar suka samu a yaki da ta’addanci.kamar yadda Muryar Yanci ta rawaito

A cewarshi yana da kyau mu bayyana cewa irin wannan maganganu daga bakunan manyan mutane musamman kamar gwamnan jaha zai iya mayar da hannun agogo baya a yaki da ta’addanci da sauran miyagu a duk fadin kasar nan.

Kakakin ya bayyana cewa sun ga wannan bidiyo, kuma zasu yi bincike a zargin karbar cin hanci da gwamnan ya yi wa Sojoji domin rundunar Sojan kasa ba ta wasa da zargin cin hanci da rashawa saboda runduna ce mai ladabi, tarbiyya da kuma tsari.