Shugaban jam iyyar APC na ƙasa Adam’s Oshimole ya taya gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje murnar nasarar da ya samiu a kotun ƙoli.

Oshimole ya bayyana hakan a matsayin nasarar ƴan jihar Kano da aka basu abinda suka zaɓa.

Ya ce hakan ya tabbatar da cewar gwamna Ganduje ne ya lashe zaɓen da aka yi a shekarar 2019.

Yayin wata ziyara da gwamnan ya kaiwa shugaban a gidansa da ke Abuja, bayan Nasarar da Alhasan Ado Doguwa ya samu a yayin zaɓen da ya gudana a ƙarshen makon da ya gabata.

Gwaman ya jinjinawa Oshimole a bisa yadda yake ƙoƙarin kai ƴan jam iyyar ga nasara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: