Miniatan sadarwa a Najerita Dakta Isa Ali Pantami ya bada umarnin rufe layukan mutanen da suka mallaki lamba sama da uku.

Cikin umarnin da aka bawa hukumar lura da layikan kira waya Najeriya NCC wanda mataimakinsa a fannin fasaha Dakta Femi Adeluyi ya sawa hannu, Pantami ya ce daga yanzu babu wanda zai sake mallakar lamba sama da uku, kuma waɗanda ke da ita ma za a rufe sauran.
Hakan dai ya biyo bayan umarnin rufe dukkan layukan wayar da ba a musu rijista ba wanda aka yi sokar a shekarar 2019.

Sannan ya ce daga yanzu idan mutum zai yi rijistar layinsa sai yayi amfani da katin ɗan ƙasa idan kuwa ɗan wata ƙasar ne zai yi amfani da Fasfo ɗinsa.

Kuma layukan da aka yiwa rijista za a sabuntasu a sakawa kowa lambar shaidar ɗan ƙasa daga nn zuwa ƙarshen shekarar da muke ciki.