A Kokarin da Rundunar yansandan jihar Katsina takeyi don ceto Wayanda akayi garkuwa dasu sun gano wani Mai suna Abubakar Muhammmad Dan Asalin jihar Kano Dake sojan gona da sunan Jami’in kwastam inda yake safarar Shinkafa.

Rundunar ta yi nasarar ceto wasu mutane ashirin da shida daga hannun masu garkuwa da jama’a domin neman kudin fansa da aka sato daga jihar Kaduna a watan da ya gabata Kakakin rundunar SP Isah Gambo ya bayyana haka ga manema labarai a Katsina a lokacin da ake holansu a gaban yan jaridu mutanen da suka hada da maza goma sha takwas da mata takwas.
A cewarsa mutunen an sato su ne daga garin Badna-Buruku da ke cikin karamar hukumar chukum da ke jihar Kaduna inda aka dauko su akan mashinan masu garkuwa da mutane zuwa cikin dajin Sabuwa da ke jihar Katsina.
Haka kuma SP Isah Gambo ya yi bayanin cewa jami’ansu sunyi nasarar ceto su ne lokacin da suke sintiri a cikin dajin dungun Ma’azu da ke karamar hukumar Sabuwa suka samu nasar kubutar da wadannan mutane wanda yanzu haka suke hannunsu kuma ana cigabab da bincike akan lamarin, bayan bincike za’a gurfanar dasu gaban kotu.

