Yarima Sulaiman Ibrahim ya ce da za a bashi dama ya zama Gwamna ko ɗan majalisa da zai yi abinda ba wani mai lafiyar ido da ya taɓa yi.

Cikin wani shiri da aka yi da shi a Matashiya TV yarima ya ce mulki ba da ido ake yinsa ba muddin mutum na da kishi zai iya yinsa ko da ba ya gani.
Wani mai larurar gani ya yi iƙirarin aiki tuƙuru matuƙar aka bashi dama don jagorantar al umma.

Yarima ya ce rashin saka maau buƙata ta musamman a harkar gwamnati ba ƙaramin koma baya bane ganin cewa suma suna da gudun mawar da za su bayar wajen tafiyar da gwamnati.

A yayin hirar ya ce Yana alfahari da kasancewasa makaho amma hakan bai sa ya ƙasƙantar da kansa ko wulaƙanta kansa ba.
Sannan ya ja hankalin jama a da su kasance masu jan mutane maau buƙata ta musamman a jiki kasancewar suna tattare da wata baiwa ta musamman a tare da su