Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labaran jiha

Ba ma buƙatar jami an tsaro masu zaman kansu a Kano, Ganduje ya ƙara jaddadawa – Mujallar Matashiya

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar jihar Kano ba ta buƙatar jami an tsaro masu zaman kansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da sabon mataimakin sufeton ƴan sanda shiyya ta ɗaya a nan Kano Sadiƙ A Bello ya kai masa ziyara a fadar gwamnati.

Gwamnan ya ce jihar Kano na aiki tuƙuru don samar da tsaro tare da haɗa kai da jami an tsaron da doka ta amince da su don aiki tare.

Yayin da yake bayani, gwamna Ganduke ya bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samar ciki har da kyamarorin tsaro da aka saka a wasu titunan jihar.

Yayin da yake nasa jawabin sabon mataimakin sufeton ƴan sanda shiyya ta ɗaya a Kano Sadiƙ A Bello ya yabawa Ganduje a bisa ƙoƙarinsa na haɗa kai da jami an tsaro don wanzar da zaman lafiya.

Ziyarar wandda suka yi a yau Laraba kuma ya samu rakiyar manyan jami an ƴan sanda ciki har da kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Habu A Sani.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: