kungiyar lafiya ta duniya W.H.O ta bayyana sunayen wasu jahohi da ka iya fiskantar barazanar cutar corona virus.
jahohin da kungiyar ta bayyana sun hada da jihar kano, lagas, Abuja, cross river, enugu sai akwa ibom da port Harcourt, sau ran sun hada da delta da bayelsa.
Babbar jami’ar kungiyar W.H.O Dhmari Naido itace ta bayyana hakan a ƙarshen makon da ya gabata a lokacin da take gabatar da jawabi a taron wayar da kan ƴan jaridu kan cutar corona virus.
Dhmari ta ƙara da cewa kungiyar W.H.O ta bayyana ƙasar najeriya a matsayin ƙasa mai mugun haɗarin kamuwa da cutar saboda yana yin sufuri tsakanin ƙasar sin da najeriya.
Daga ƙarshe ta bayyana cewa kungiyar na aiki ƙarfafa tsaro a iyakokin shiga najeriya da kuma taimakawa dan ganin wannan cuta corona virus bata samu damar ɓullowa a najeriya .
Kima nin mutane 30 ne ƴan ta da ƙayar baya suka kashe tare da yin awan gaba da wasu mata da ƙananan yara.
Maharan sun yi wannan kisa ne a wani hari da suka kai a ƙauyen Auno dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
haka kuma ajiya litinin mayaƙan suka sake afkawa ayarin matafiya sakamakon rufe hanyar da ta haɗa Maiduguri zuwa Damaturu.
Zuwa yanzu dai ba a bayyana adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu a saka makon harin, sai dai ana ƙyautata zaton mata da yara sune harin yafi shafa.