Gwamnatin jihar Lagos ta musanta rade radin da ake yadawa cewa wani dan asalin kasar chana da ke zaune a jihar yana dauke da cutar corona virus.
Kwamishina lafiya na jihar Akin Abayomi shine ya musanta zargin a jiya, yayin da ya wallafa a shafinsa na tweeter, in da yace wanda ake zargi dan asalin kasar chana dake a unguwar gowon a karamar hukumar alimosho cewa wannan labari ne mara tushe bari makami bare makama.
Mista Abayomi yace zuwa yanzu ana gudanar da bin cike dan tabbatar da rashin ingancin wannan labarai.
A cewar sa zuwa yanzu babu labarin bullar wannan cuta a fadin najeriya.
Cutar Corona virus cutace da ta barke a garin wuhan dake kasar chana wanda ta yadu zuwa sassan kasa she 25 in da yanzu ake da rahotan a kalla mutane 800 suka mutu saka makon wannan cutar yayin da mutane 37000 suka kamu da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: