Hakan ka iya faruwa ne biyo bayan yadda
Kungiyar direbobi masu dakon Mai Reshen jihar sun fara yajin aikin Gargadi.

Yajin aikin da suka shiga ya biyo bayan zargin da suke na irin tsangwama da suke fuskanta daga hukumar Kwastam ke musu.
Shugaban kungiyar Direbobin Alhaji Sa’idu Al’amura shine ya sanar da fara yajin aikin a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa.

Inda yace sun yanke wannnan matsaya ne don nuna damuwarsu kan irin cin zarafin da hukumar Kwastam ke yi wa direbobi masu dakon Mai a kwaryar Birnin kano.

Sai Alh Sa’idu yace wannan yajin aikin na Gargadi ne Wanda suka fara a jiya talata, don kawo karshen cin tsangwama da suke fuskanta.
Madogara
Solace Base