Ministan sadarwa a Najeriya Dakta Isa Ali Pantami ya ce bai kamata malamai su da sauran al umma su soki ƙidirin gqamnati na haramta bara a titi ba.

Dakta Pantami ya bayyana hakan ne a yyin da yake gabatar da wata maƙala yayin wani taro da aka shirya a kwalejin ƙirƙira ta Kano Polytechnic a jiya juma a.
cikin wata sanarwa da babban sakataren watsa labarai gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar a yau, Ministan ya ce bara ba addini bace sannan ba ɗabi a ce mai kyau ba abinda ya fi kamata shi ne, alarammomi su zauna da gwamnati don ganin an magance matsalar tare.

Pantami ya bayyana cewar ciyar da ƴaƴa alhaki ne na iyayen yara ba a barsu suna yawon bara a titi ba.

Sannan ya jinjinawa gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a bisa yadda yake ƙoƙarin samar da hanyoyin koyar da sana o i ga matasa da kuma sauran ci gaba a Kano.
Gwamnatin Kano dai ta sanar da haramta bara a kan titi tare da hukunta iyayen yaran da aka samu suna bara ta hanyar gurfanar da su a gaban kotu.