Hukumar Dake kiyaye Hadura ta kasa ta haramta Daukan Fasinjoji Biyu a gaban mota, a fadin Kasar Nan.

Mai magana da yawun Hukumar CPEO Bisi Kazeem shine ya tabbatar da hakan a yau juma’a a lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) A Abuja.

Ya kuma kuma bayyana cewa hukumar Tana nan Kan bakanta cewa lallai masu amfani da motoci da su kiyaye dokokin toki don kare kai daga fadawa Hadura.

Daga karshe ya bayyana cewa dokar diban Fasinjoji da suka wuce iyaka a bayyane yake yanzu zai fara aiki gadan gadan don kiyaye Hadura a fadin kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: