Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Mallam Isma ila na Abba Afakallahu ya bayyana cewar za su hukunta duk wanda aka tabbatar ya yi bidiyon tsaraici da gangan.

Yayin wata tattaunawar da mujallar Matashiya ta yi da shi ta wayar salula, Afakallahu ya ce suna kan bincike don tabbatar da sahihancinsa da kuma manufar yinsa.
Mujallar Matashiya ta nemi jin ko hukumar na da wata ɗoka da ta tanada kan waɗanda suka yi bidiyon tsaraici?

Afakallahu ya ce “E tabbas abinda doka ta ce shi ne kwace lasisin wanda aka samu da hakan matuƙar an tabbatar cewar yayi da gangan, idan kuwa an yi bisa rashin sani ko a ɗauki mutum bai sani ba, wannan kuma wani abu ne daban”

Ya ƙara da cewa hukumar ba za ta lamunci zubar da ƙimar masana antar ba domin su masu faɗakarwa ne.
“Aikin hukumar mu ne tabbatar da an bi tsari na al ada da kuma addini don haka ba za mu bari wani ya rusa mana wannan tsari ba” Afakallahu.
A yau Alhamis ne kuma shugaban hukumar suka fita ran gadi tare da muƙarrabansa don tabbatar da wuraren da ake sana ar ba su kaucewa ƙa ida ba.
Ko da mujallar Matashiya ta tambayeshi shin dama aikin hukumar na daga cikin bibiyar aikin da ake yi a waje wanda ya shafi sana ar waƙa da wasan hausa?
Afakallahu ya ce ” ai dama aikinmu shine ran gadi, ba aiki ne na zama a ofis ba, kuma fitar da muka yi yau mun zagaya wurare da dama sannan mun tsawatar a inda muka ga ana yin ba dai dai ba”.