Tsohon sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi ll ya shaƙi iskar ƴanci bayan da kotu ta yi umarni ga jami an tsaro da su sakeshi don bashi damar walwala.

Tun bayan da aka kai sarkin garin awe da ke jihar Nassarawa, a safiyar yau mahaifiyarsa ta halarci garin.

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El rufa i ma ya halarci garin Awe a safiyar yau juma a.

Sarkin ya bar garin Awe da misalin ƙarfe 4:27 na yammacin juma a tare da rakiyar gwamnan Kaduna Mallam Nasir El rufa i.

Kotu ta yi umarni da a saki sarkin tare da bashi damar zuwa duk inda yake so banda jihar Kano.

Lauyoyin Mallam Muhammadu Sanusi ll sun yi ƙarar Sufeton ƴan sandan najeriya, da shugaban hukumar tsaron farin kaya da DSS da kwamishinan shari a na jihar Kano da ministan shari a a Najeriya bisa kamun talala da aka yiwa sarkin bayan an warware rawaninsa.

Kuma ya bar garin Awe bayan ya jagoranci sallar juma a a garin kamar yadda mazauna garin suka roƙeahi da hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: