Fadar gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da rasuwar shugaban ma aikatan fadar mallam Abba Kyari a daren jiya.

Sanarwar da mataimakin na musamman ga shugaban ƙasa kan kafafen yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar, ya ce za a sanar da lokacin da za a yi jana izarsa.

