Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari,ya bada umurnin rufe babban birnin jihar Katsina, sakamakon samun mutum biyu da cutar Corona virus a cikin garin Katsina.

Masari ya bayyana hakan a lokacin da yake wa al’umma jihar Katsina jawaabi sakamakon bullar cutar.

Gwamna Masari ya kara da cewa daga ranar talata da karfe bakwai, na safe ba shiga ba fita.
Haka kuma sauran kananan hukumomi da ba a rufe su zauna garin su, ba maganar zuwa wata karamar hukumar.

Masarin ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su zamanto masu bin wannan doka, Kuma duk wanda ya karya ta doka za ta hau kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: