Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gana da Yan kasuwa kan hauhawar farashin kayan abinci Musamman a wannan wata na Ramadan.
Gwamnan ya gana da Yan kasuwan ne a dakin taro na gidan gwamnatin jihar, a yammacin ranar laraba.
.
cikin sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamman Abba Anwar ya fitar ya rabawa manema labarai.
Sanarwar tace gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya saurari korafe korafen Yan kasuwa kan irin halin da ake ciki na zaman gida don gudun yaduwar Annobar Corona Virus.
Haka zalika gwamnan yayi Alkawarin Ganawa Da Shugabanin rukunin Kamfanoni Dangote Alhaji Aliko Dangote da takwaransa Abdussamad Isyaka Rabi’u mai Kamfanin BUA don ganin yadda za’a shawo kan matsalar hauhawar farashin kayan abinci Musamman a wannan lokaci na azumi.
Ganduje yayi Alkawarin sanar da Yan kasuwan duk yadda suka tattauna da masu Kamfanonin.