Wannan jawabi yazo ne ta bakin Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, bayan ya rantsar da wani kwamiti da zai aiwatar da shirin gwamnatin tarayya na daukar mutum 1,000 aiki a kowacce karamar hukuma 774 dake Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, fadar gwamnatin Najeriya ta ce an rantsar da kwamitin ne bayan Shugaba Buhari ya amince da fara gudanar da shirin na tsawon wata uku.

Ta ce an kirkire shi ne da zummar rage wa ‘yan kasa radadin da annobar korona ta jefa su ciki.

Kwamitin zai kasance karkashin jagorancin babban darakta a ma’aikatar samar da aikin yi Dr. Nasiru Ladan, sai kuma wakilai daga ma’aikatun kudi da lafiya da aikin gona da sufuri da ruwan sha da ma’aikatar ayyuka da gidaje.

Idan shirin ya tabbata, gwamnatin Najeriya za ta bai wa mutum dubu 774,000 aikin yi a cikin wata uku.
Kamar yadda majiyar mu ta muryar yanci ta rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: