Majalisar dinkin duniya da hukumar lafiya ta duniya (WHO)ta tura jami’ai 3,000 jihar Kano don bada tallafi a kan Cutar Covid 19.

Shugaban kwamitin yaki da cutar na Kasa, kuma Sakataren gwamnatin Tarayya Boss Mustapha, shine ya sanar da hakan yayin jawabi a garin Abuja a yammacin Juma’a.
Boss Mustapha, ya ce hukuncin da gwamnatin tarayya ta dauka ya fara kawo nasara a jihar Kano.

Gwamti ta mayar da hankali sosai wajen horar da jami’an kiwon lafiya da suka hada da likitoci, malaman jinya har da masu goge-goge ta yadda ba za su kwashi cutar ba.

Haka kuma akwai tsare tsare da salo daga fadar shugaban kasan wanda zai bada gudumawa a kowanne lokaci.
Duk da yadda masu cutar a jihar kano na kara hauhawa, amma kuma hakan na nuna matukar nasara ne ta yadda ake zakulo masu cutar tare da killacesu.
Hoto: Muryar yanci