Gwamnatin jihar Kano ta bakin hukumar sauraron korafe-korafen jama’a da kuma yakar cin hanci da rashawa ta cimma yarjejeniya da kungiyar masu sarrafa shinkafa ta kasa dake jihar,
kan kayyada farashin buhun shinkafar mai nuyin kilogiram 50 kan naira dubu 16.

Rahotanni sunce an rattaba hannu kan yarjejeniyar kayyade farashin buhun shinkafar a hedikwatar hukumar sauraron korafe-korafen al’ummar ta Kano,

bayan ganawa tsakanin shugabanta Barista Muhuyi Magaji Rimingado da shugaban kungiyar masu sarrafa shinkafa na Najeriya, reshen Kano Alhaji Muhammad Abubakar Maifata.

A karkashin yarjejeniyar, kungiyar masu sarrafa shinkafar za su rika shigar da tirela 30 makare da shinkafa a kowane mako, inda za a rika saidawa shagunan saida kayayyaki a sassan jihar kan farashin naira dubu 15, 500 bisa kowane buhu guda, yayinda su kuma shagunan za su rika saidawa jama’a buhun shinkafar kan farashin naira dubu 16,000.

Majiyar mu ta Rfi ta rawaito cewa yarjejeniyar kayyade farashin shinkafar tace ba za a saidawa mutum guda sama da buhuna 2 ba, a wuraren da aka yarjewa saida shinkafar.
Wannan na wani Mataki ne da gwamnatin ta dauka na rage radadin zaman gida sakamakon Bullar Cutar COVID 19.

Leave a Reply

%d bloggers like this: