Kotun majistrate mai lamba 82 dake zamanta a Rijiyar Zaki, karkashin mai shari’a Musa Ibrahim Umar Fagge, tayi umarnin da a kamo mata shugaban karamar hukumar Kumbotso Alhaji Kabiru Ado Panshekara,
bisa kin halattar kotun da yayi,
Tun da farko.
hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar kano karkashin Jagorancin Muhuyi Magaji Rimin gado,ta gurfanar dashi a gaban kotun
Hukumar dai na tuhumar shugaban Karamar Hukumar kumbotso da karkatar da kayan tallafin da gwamnati ta bayar a rabawa al’ummar yankin Kumbotso.
Wanda ake zargin an rabawa manyan jami’an Kananan Hukumar ne.
Laifin dai ya sabawa kundin tsarin Hukumar sashi na 22/23 da 26.