Wani mummunan hadari yayi sanadiyar mutuwar mutane biyar yayin da Biyar aka garzaya dasu asibiti.

Hadarin ya faru ne jiya a hanyar Rimin gata dake karamar hukumar Ungogo a jihar kano.

Jami’in hulda Da jama’a na hukumar kashe gobara Alhaji sa’idu Muhammmad ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun samu Rahoton hadarin ne ta bakin malam Usman Aminu Iguda da misalin karfe 7:18

A cewarsa kakakin Rahoton da suka samu ya tabbatar musu da cewa taho mu gama akayi tsakanin Mota Golf
Mai lamba KMC-828 ZV da wata babbar mota kirar Tifa. bayan suna Mugun gudu.

Ya kuma kara da cewa Bayan sun samu Rahoton hadarin jami’an sa suka garzaya gurin Dan bada agajin gaggawa yayin da suka tarar mutane 5 sun mutu inda aka garzaya da mutane biyar asibitin kwararru na Murtala. Don basu kulawa ta musamman.

NAN/ daily trust

Leave a Reply

%d bloggers like this: