DAGA RABIU SANUSI KATSINA.

An Bukaci al’ummar da ke zaune a yankunan da matsalolin tsaro ya addaba, da su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri dan a samu damar dakile ma su tada kayar baya a wa su sassa na jihar katsina.
babban mai ba gwamnan jihar katsina shawara kan harkokin tsaro Alh, Ibrahim Ahmad, shine ya yayi wannan Kira a yayin wata Ganawa da wakilin mu na katsina ranar litinin.

Hon Ibrahim ya bayyana cewa a kokarin gwamnatin Rt Hon Aminu Bello Masari na kawo zaman lafiya a fadin jihar yasa mai girma gwamna ya bukaci taimako na musamman daga gwamnatin tarayya, kuma cikin yardar Allah an samu nasarar aiko da jami’an tsaro na musamman.

Haka zalika hon Ibrahim yayi Kira ga Al’umma da a tabbatar da cewa ana sanar da jami’an tsaro wani abu dake faruwa.
A cewarsa jami’an tsaro babu abin da su ke bukata face hadin kan mazauna yankunan da abin ya ke faruwa, inda ya bayyana wannan ne kadai hanyar da za su iya cimma ma su laifin cikin sauki.
Ibrahim Ahmad ya kuma jinjina ma mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa amsa kukan da al’ummar jihar katsina takai kan matsalar tsaro kuma ta amsa ta turo dauki.
Haka zalika ya nuna godiyar shi ga mai girma gwamna akan yunkurin shi na samar da zaman lafiya ga al’ummar jihar katsina, haka zalika ya yaba da irin kokarin jami’an tsaro da su ke fafatawa a wannan yunkuri na dakile Yan ta’adda a arewa maso gabas da yamma na kasar nan.
Daga karshe ya yi albishir ga manoman yankin da su kara addu’a dan idan Allah ya yarda za su cigaba da ayukan su na gona kamar yadda aka saba yi.