Daga Ummi Aliyu
Jami’an tsaro na Civil defence sun cafke wasu Mutane biyu bisa zargin su da yiwa wata yarinya mai Shekaru 11 Fyade a karamar hukumar Ajingi.
Majiyar mu ta Kano Focus tanrawito cewa Hukumar dai sun yi holen Wanda a ake zargin ne a gaban manema labarai a jiya talata.
Mai magana da yawun Hukumar ibrahim Idris Abdullahi duk Wanda ake zargen sun hada da Aminu Muhammmad Wanda ake Kira da Skylolo mai shekaru 35, sai Abubakar Safiyanu Wanda ake Kira Da RKelly mai Shekaru 40.
Abdullahi ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin za’a gurfanar dasu gaban Shari’a bayan an gama bincike.
Daga karshe yaja hankalin iyayen yara da su dage wajen kula da Yayansu domin karesu daga hannun Bata gari, da sauran masu aikata mugun laifuka.