Gwaman Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa Kwamishinoninsa sauye sauyen Ma’aikatu tare da rantsar da Kwamishinan Ayyuka.

Ganduje ya Rantsar da kwamishinonin Jim kadan bayan Kammala zaman majalisar zartarwar jihar a yau laraba.

An dai Rantsar da Idris Garba Unguwar Rimi a matsayin sabon kwamishinan Ayyuka da cigaba.

Wayanda aka sauya musu Ma’aikatu sun hadar da:

1) Mahmud Muhammad Dan Santsi daga ma’aikatar Kasuwanci zuwa ma’aikatar Gidaje da Sufuri.

2) Barrister M.A. Lawan daga ma’aikatar Gidaje da Sufuri zuwa Ma’aikatar Sharia.

3) Barrister Ibrahim Mukhtar daga ma’aikatar Shari’a zuwa Ma’aikatar Kasuwanci.

Da yake jawabi gwamman Kano yaja hankulansu da su sanya harkokin cigaban jihar Kano a gaba kamar yadda ya daura musu nauyi.

Ya kuma yi Kira da Kwamishinonin da su cigaba da bin Dokokin kare Kai daga Annobar Covid 19.

PR.

Leave a Reply

%d bloggers like this: