Hukumar dake lura da ababen hawa ta jihar Kano KAROTA tace sai da kwamitin dake yaki da masu Kasa Kaya ba bisa ka’ida ba Karkashin Jagorancin shugaban KAROTA Baffa Babba Dan Agundi suka bawa dukkanin masu Rumfuna dake kan Hanya Wa’adin Tashi har na tsawon wata 6 kafin a tashe su.

Wannan na kunshe ni cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da jama’a na hukumar KAROTA Abubakar Nablusi K/naisa ya fitar ya bayyana cewa gwamnati bazata lamunci dukkanin masu kasa Kaya akan hanya ba.
Wannan ya biyo bayan Zanga zangar da wasu daga cikin yan kasuwar Sabon gari suka fito a safiyar yau litinin.

Nablusi ya kara da cewa tsohuwar gwamnati ta Samar da wuraren da Yan kasuwar zasu koma, a unguwar bachirawa dake Karamar hukumar Ungoggo, da kuma wata a rijiyar zaki kan titin Gwarzo dake Karamar hukumar gwale.

Ya kuma bayyana cewa sun karbi korafe korafe kan yan kasuwar da kayansu suka bata a lokacin da aka Gudanar da Rusau dasu shigar korafi a ofishin yan sanda dake sabon gari.
Daga karshe yaja kunnen dukkanin masu kokarin tayar da hankulan Al’umma da sunan zanga zanga zasu fuskanci fushin hukumar dama sauran jami’an tsaro.
Kwamitin dake yaki da masu Rumfuna ba bisa ka’ida ba sun hada da:
Baffa Babba Dan Agundi da sauran jami’an tsaro.
Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli REMASAB.
MD na kasuwar Sabon gari.
MD na hukumar tsara birane na jihar Kano KNUPDA da sauran shugabannin yan kasuwa dake kasa Kaya.