Wata kotu a jihar Legas da ke sauraron karar fyade da rigimar iyali na musamman ta yankewa wani ‘dan acaba mai shekaru 37 daurin shekaru 20 a gidan kurkuku.

kotun dake a garin Ikeja ta kama Emmanuel Idoko da laifin yiwaa ‘yar cikinsa mai shekara 12 da haihuwa fyade.

Da yake zartar da Hukuncin Alkali Sybil Nwaka ya ce masu kara sun gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa Mista Emmanuel Idoko ya aikata wannan laifi.

Alkalin ya ce: “An samu wanda ake kara da laifin lalata ta hanyar tarawa ba tare da izni ba, wanda hakan ya sabawa sashe na 261 na dokokin laifin jihar Legas na shekarar 2015.”

Babajide Boye wanda shi ne Lauyan da ya tsayawa yarinyar da aka boye sunanta, ya bayyana cewa uban na ta ya aikata wannan laifi ne a gidansu da ke Oworoshoki, Legas tun a Shekarar 2017.

Akalla mutane hudu ne su ka bada shaida a kan Idoko, ya aikata laifin yayin da shi kadai ne ya bada shaida domin ya kare kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: