Babbar kotun musulunci da ke da zama a Hausawa filin hockey ta yanke hukuncin kisa ga matashin da yayi wani sauti da muryarsa a ciki yayi ɓatanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.

An yankewa Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya ne bayan da aka kamashi da aikata mummunan laifin waƙe na ɓatanci ga Annabi S.A.W.
Mai shari a Khadi Aliyu Muhammad Ƙani ne ya yanke hukunci a bisa laifin da aka kama matashin ya aikata tun a watan Maris ɗin da ya gabata.

Matashin dai yayi saƙon murya ne wadda ta sanya musulmi yin Allah wadai tare da ƙoƙarin ganin an gurfanar da shi a gaban kotu don girbar abinda ya shuka.
