Mutumin dai ya bayyana abinda matar tasa ta yi a matsayin leken asiri a don haka yake duba yuwuwar makata a gaban kotu.

Wani mutum a ƙasar saudiyya ya ce yana duba yuwuwar kai ƙarar matara gaban kotu a bisa bincike da ta yi masa a dandalin whatsapp ba tare da saninsa ba.
Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewar matar ta nemi ya saketa bayan ta sauke duk saƙonnin da ke whtasapp ɗinsa tare da hotuna da bidiyon da ke ciki.

Haka kuma matar ta nemi ya bayyana tallafin da zai bata kafin a raba auren.

Tsawon watanni tara matar tana masa bincike a Whatsapp ba tare da saninsa ba.