Wasu yan bindiga a ranar Juma’a sun kai hari ofishin yan sandan unguwar Ikolaba, Ibadan, birnin jihar Oyo.

Da yake Tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar yan sandan jihar Oyo, Gbenga Fadeyi, ya bayanawa Channels TV cewa ya samu labarin harin misalin karfe 9 na dare amma bai da tabbacin barnar da akayi ba.

Fadeyi ya kara da cewa zuwa yanzu an tura karin jami’ai ofishin yan sandan Ikolaba yayinda ake cigaba da gudanar da bincike.

Yan bindigan sun hallaka dan sanda daya kuma da dama sun jikkata.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan kashe dan sandan, sun kwashe makaman da ke ofishin yan sanda.

Leave a Reply

%d bloggers like this: