Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar yan sanda a jihar Kano sun samu gawar wata mata da ake zargin mijinta ya kulleta cikin daki tsawon kwanaki uku a jihar Kano.
An samu gawar wata matar da mijinta ya kulle tsawon kwana 3 a Kano

Mujallar Matashiya ta zanta da yar uwar marigayyar inda take cewa auren zumunci akayiwa mamaciyar takara da cewar daman shi maigidan marigayyar yadade yana azabtar da ita inda yake fita daga gidan yarufeta da mukulli.

Shidai wannan lamari yafaru a unguwar mariri dake cikin kano marigayyar take dauke da juna biyu kuma nakuda yakamata ayayin da babu maikawowa marigayyar agaji sakamakon gidan dake rufe.
Makotan marigayyar sunce su ko almajiraima basa shiga gidan inda kullum gidan arufe yake kuma babu inda take shiga acikin unguwar, sunce maigidan yazo yanemi agaji makwabtan nashi bisa wari dayaji gidan yanayi bayan anje anbude gidan akaga marigayyar harta fara tsotsa da kuma wari.
Sai dai mai magana da yawon yansanda reshen jahar kano DSP Abubakar Haruna ya tabbatar da faruwar al’amarin indayace sun mika maigidan marigayyar zuwa sashin bincike na manyan lefuka domin tsawaita binciken kan faruwar lamarin.