Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta cafke mutane 45 da ake zarginsu da laifin garkuwa da mutane da mallakar miyagun makamai a sassa daban daban na jihar.

Daga cikin wadanda aka kama, akwai mai shekaru 40 wanda ake zargin ya kware wajen safarar makamai ga ‘yan kungiyar tada kayar baya.

Jihar Borno ta dade tana fuskantar matsalolin tsaro, inda aka kashe mutane da dama, ya yin da dubunnai suka rasa muhallansu.

A yayin da jami’an tsaro ke fafutukar dai-daita lamuran tsaro a jihar, a hannu daya kuma ana aikata wasu laifukan a sassa daban daban na jihar.
Amma rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno ta ce ba za ta sarara ba har sai ta wanzar da zaman lafiya da cafke masu aikata munanan laifuka a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: