Dakarun Sojin Najeriya karkashin atisayen Operation Sahel Sanity, sun damke yan bindiga akalla 150 kuma sun hallaka daya a jihar Zamfara.

Mukaddashin diraktan harkokin yada labarai rundunar, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a Faskari, jihar Katsina ranar Talata.

Onyeuko ya ce Sojin sun gano wata mabuyar yan bindigan dake Gadan Zaima inda suka kama su.

Ya kara da cewa yan bindigan da aka damke suna hannun yan sanda kuma ana cigaba da bincike kansu.

Yace: “A ranar 23 ga Agusta, 2020, rundunar Soji sun aiwatar da binciken leken asiri kuma suka kai hari wani wajen hakar ma’adinai dake hanyar Gadan Zaima-Zuru a karamar hukumar Bukuyyum na jihar Zamfara inda yan bindiga ke boyewa.”

“Yayin harin, dakarun sun damke mutane 150 kuma sun kwace bindigogin gargajiya 20. An kashe daya daga cikinsu yayinda yake kokarin guduwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: