Najeriya ta aika wa gwamnati da mahukuntan kasar Ghana da sakon jan kunne sakamakon muzgunawa dan Najeriya da ƙasar ke yi.

Ministan yada Labarai, Lai Mohammed yayi wannan gargadi ta cikin wani sako da ya fitar.

sanarwar da Lai Mohammed ya fitar ya ce yanzu haka sakon ya isa ga gwamnatin Ghana har kwace ofishin jakadancin Najeriya tayi dake titin Barnes dake babban birnin kasar, Accra.

sannan kuma ta sake zuwa ta rusa wani gini mallakin gwamnatin Najeriya dake titin Julius Nyerere a kasar.
” Bayan haka, shekaru uku kenan duk shekara sai kasar ta dawo da daruruwan dan Najeriya gida wai basu da takardun zama a kasar ko kuma basu shiga ƙasar bisa ka’ida ba.

” Sannan kuma mahukunta a kasar na bi suna garkame shagunan dan Najeriya babu gaira babu dalili, bayan ta zabga musu kuɗin haraji.

Kazalika gwamnatin ta yi wa dokokin zaman kasar garambawul da yanzu ta tsawwala kudin sabunta lasisin zama a Ƙasar duk shekara wanda a Najeriya dan ƙasar Ghana naira 7000 kacal yake biya kuɗin zaman kasar.

Haka kuma da gangan mahukuntar kasar suke tsananta shari’a akan Dan Najeriyan da ya fada hannun su.

Zuwa yanzu akalla mutum 200 dan Najeriya na kulle a gidan Kaso na Kasar.
A daga karshe Lai Mohammed yace gwamnati bazata lamunci irin cin zarafin da ake wa alummarta ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: