Tsoffin malaman makarantun firamare tare da na kananan hukumomi a jihar Delta da suka yi murabus, sun fito zanga-zanga a ranar Talata.

Sun mamaye kofar gidan shiga gwamnatin jihar inda suke bukatar a biya su hakkokinsu wanda gwamnatin Gwamna Ifeanyi Okowa ta hanasu.
Masu zanga-zangar rike da takardu dauke da bayanai sun hana shige da fice a gidan gwamnatin.

Sun hana dukkan jami’an gwamnati da masu ziyara shiga gidan.
Sun zargi gwamnan jihar da nuna musu halayyar mugunta a kan yadda yayi shiru ya hana su hakkokinsu.

Kamar yadda masu ritayar suka bayyana suka fito suna dauke da kayayyakin girki, tabarma da sauran kayayyakin, sun ce da gangan Gwamna Okowa ya hana su kudadensu tun bayan da ya hau kujerarsa.
Wasu kuwa sun baza tabarminsu a gaban kofar shiga gidan gwamnatin yayin da jami’an tsaro suka hana su shiga.