Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Labarai

Yan bindiga sun sace wani jami’in tsaron farin kaya na DSS

Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun sace wasu mutane a kan tintin rigacikun zuwa Afaka a jihar Kaduna.

Cikin mutanen da aka sace akwai wani jami’in tsaron farin kaya na DSS bayan sun sace wasu fararen hula.

An gano motar jami in da jini tare da harbin bindiga jikinta a cikin daji, sai dai ba a tabbatar da cewar ko an hada da ƙaramar ƴarsa wadda suke tare ba.

Wata majiya ta ce yan bindigar sun nemi iyalan jami in su bada naira miliyan 100 kafin su sakeshi.

Hakan na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun sace wani jami in tsaron farin kaya a katsina, sukakarbi kudi naira miliyan 5 sannan suka kashe shi.

Ko a makon da ya gabata  sai da yan bindiga suka sace wasu alƙalai a jihar Zamfara

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: