Akalla mayakan kungiyar boko haram 13 ne suka mika wuya ga rundunar sojin najeriya a jihar Borno.

Mayakan boko haram 13 tare da mata da yayansu guda 23 ne suka mika kansu ga rundunar sojin a karamar hukumar bama.

Mai lura da al amuran sadarwa manjo janar John Enenche ne ya bayyana cewar, mayakan sun mika wuya ne sakamakon luguden wuta da jami an tsaron ooperation lafiya dole suke a yankin gabashin kasar.

Ya kara da cewa mayakan tare da iyalansu suna karbar kulawar magunguna a sashen lura da marasa lafiya na rundunar soji.

Sannan kuma suna cigaba da bincike a kan yan boko haram din da iyalansu kafin su dauki mataki na gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: