Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce ya sha fama da irin hare-hare da ake kai masa ba tun yanzu ba, kuma hakan ba zai sa ya fasa gudanar da ayyukansa ba.

Ya ce tun yana matsayin kwamishina yake fama da hare haten ƴan tada ƙayar baya.
Rundunar sojin najeriya ta ce tana goyon bayan gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum kan mayar da yan gudun hijira muhallinsu.

Mukaddashin shugaba a fannin yada labarai kanal sagir musa ne ya sanar da hakan bayan gwamnan ya jaddada kudirin cigaba da kai ziyara tare da mayar da yan gudun hijira muhallinsu.

Hakan ya biyo bayan harin da aka kaiwa gwamnan karo na uku wanda ake zargin kungiyar boko haram c eke da alhakin kai harin.
Gwamana Babagana Umara Zulum ya tabbatar da cewar harin bai tayar masa da hankali ba sakamakon ya taba fuskantar hakan a baya.
Cikin wata tattaunawa da BBC suka yi da gwamna yace ko da mayakan boko haram za su cigaba da kai masa hari ba zai fasa zuwa wajen yan gudun hijirar ba.
Gwamnna ya jinjinawa jami an tsaron da suke rakiyarsa wanda ya tabbatar da cewar sun yi matukar kokari wajen dakile harin masu tada kayar baya.