Shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da ƙarin albashi ga malaman makaranta a ƙasar.

Jawabin hakan ya fito daga bakin misitan ilimi a ƙasar mallam Adamu Adamu.

Ya ce an fito da sabon tsarin albashin ne don ƙarfafa gwiwar malamai a ƙasar.

Haka kuma an ƙara yawan shekarun ritaya ga malaman daga shekaru 35 zuwa shekaru 40.

Zuwa lokacin da muke kammala wannan labara ba mu samu rahoton yadda tsarin zai kasance ba.

A dukkanin ranar 5 ga watan Oktobar kowacce shekara, majalisar ɗinkin duniya ta ware don bikin tunawa da malamai a duniya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: