Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya buƙaci al ummar jihar Kano da su zauna lafiya tare da kaucewa tada hankali.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron ƙungiyoyin al umma don tabbatar da muhimmancin zaman lafiya wanda aka yi a jiya Alhamis.
Ganduje ya bada misalin abinda ya faru a wasu jihohin wanda hakan ya haifar da ƙaƙaba dokar hana fita wamda ya ce baya so hakan ta faru a jihar kano kasancewar ma ba a daɗe da cire dokar kulle a kan Korona ba.

“Kun ga dai abinda zanga zangar take haifarwa a wasu jihohin ƙasar nan, ga kuma makomar da suka shiga na dokar hana fita, ya kamata wannan ya zama izina a garemu” Inji Ganduje

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na iya ƙoƙari don ganin an daƙile duk wata hanya da zata kawo hargitsi a jihar, misalin abinda ya faru a unguwar ƙofar mata da sabon gari, a cewar Gwamna Ganduje, sun yi ƙoƙari don shawo kan al amarin don tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano.
Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Mallam Abba Anwar ya fitar a yau gwamnan ya shawarci al ummar jihar Kano da su kasance maau kaucewa duk wata hanyar da za ta iya haifar da fitina a jihar Kano don amsa sunanta a matsayin jihar zaman lafiya.