An saka dokar hana fita a jihar Adamawa bayan an buɗe ɗakin tara abinci a jihar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya fitar da sanarwar bayan samun wasu ɓata gari da suka ɓalle ɗakin ajiyar kayan abinci a jihar.

Sanarwa ta ce yan sanda a jihar haɗin gwiwa da wani kwamiti ne zai yi aiki don ganin mutane sun bi dokar.

Rundunar ƴan sandan jihar ta buƙaci al ummar jihar da su mutunta dokar don faɗawa komar hukumar.

Haka kuma sun ce ba za a sanya idanu mutane suna yin abinda suka ga dama ba musamman wanda ya ƙetara iyaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: