Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya Farfesa Mahmood Yakubu ya naɗa Air Vice Marshal Ahmed Mu azu mai ritaya a matsayin shugaban hukumar na riƙo.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Farfesa Mahmood a matsayin shugaban hukumar a karo na biyu.

A yau wa adin shugaban ya cika kuma zai bayyana a gaban majalisar dattijai don tantancewa kafin zamansa shugaban hukumar a karo na biyu.

Za a sake rantsar da shi a matsayin shugaban hukumar bayan majalisar ta amince da shi don jagorantar hukumar a karo na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: