A yau Talata majalisar dokoki a Najeriya ta amince da naɗin Farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta karo na biyu.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya amince da sake naɗa farfesa Mahmud Yakubu a matsayin shugaban hukumar karo na biyu kuma daga bisani majalisa ta tantanceshi tare da tabbatar da shi.

Farfesa Yakubu dai shi ya jagoranci zaɓen shekarar 2019 a Najeriya, kuma wannan ne karo na biyu da shugaban ƙasa ya kuma bashi damar sake shugabantar hukumar.

Tun a ranar 26 ga watan da ya gabata aka kafa kwamitin da zai tantanceshi kuma kwamitin ya miƙa rahotansa.

Wannan ke nuni da cewar Farfesa Mahmud Yakubu zai sake jagorantar zaɓen sherara 2023 mai kamawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: