Kwamishinan yaɗa labaran gwamnatin Kano Mallam Muhammad Garba ya ce gwamnatin Ganduje ba ta taɓa kama ɗan jarida ba.

Muhammad Garba ya bayyana hakane a yayin da yake jawabi wajen taron murnar cika shekaru huɗu da kafuwar Freedom Radio.
Ya ce duk irin suka da ake yi akan daidai da akasin haka gwamnatin na kauda kai a kan dukkan abinda ake mata.

Mallam Muhammad Garba ya buƙaci yan jarida da su kasance masu gudanar da aiki a cikin tsari tare da zaƙulo hanyoyin da gwamnati za ta bi ta gyara ayyukanta.

“Ko da anyiwani abu na ba dai-dai ba mukan ƙoƙari mu danne tare da nusar da kafar yaɗa labarai cewar ga kuskurenta.
Ba ma faɗa da ɗan jarida ko kafar yaɗa labarai” inji Muhammad Garba.
Sannan ya bayyana cewar a matsayina na ɗan jarida, ba zai so a kowanne lokaci a ke goyon bayan gwamnati ba ko yin abinda gwamnati take so.